
Rahotanni daga fadar White House ta kasar Amurka na cewa, shugaban kasa, Donald Trump na ci gaba da matsawa Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu akan ya dakata da yakar Falasdinawa.
Rahotan yace Shugaba Trump har ta kai ga ya gayawa Benjamin Netanyahu cewa ko dai ya daina wannan yaki ko su yanke duk wata hulda dashi.
Benjamin Netanyahu dai ba zai so hakan ba saboda mafi yawa kasar Amurka ce ke sayar musu da makamai.
Saidai a wata majiyar an ji cewa, Benjamin Netanyahu na fadar zasu ci gaba da yakin kuma zasu samu nasara ba tare da taimakon kasar Amurka ba.
Hakanan a wani Rahoto me kama da wannan, kasashen Ingila, Faransa da Canada sun yi barazanar daukar kwakkwaran mataki muddin Israela bata dakata da sabbin munanan hare-haren da take kaiwa a Gaza ba da kuma janye hana kai kayan agaji da ta yi.