Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan kudi da tattalin Arziki, Wale Edun ta bayyana cewa, zata kawo saukin rayuwa ga ‘yan Najeriya ta hanyar saukaka farashin kayan abinci.
Ya bayyana hakane bayan ganawa da shugaban kasar ranar Lahadi a Legas, yace gwamnatin zata samar da karin ayyukan yi a shekarar 2025 bayan samun saka hannun jari daga kasar Saudi Arabia
Minista Edun bai dade da dawowa daga kasar Saudi Arabia ba biyo bayan ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai kasar kan maganar zuba jari a Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa sun dawo da albishir daga kasar Saudi Arabia cewa za’a saki karin ayyuka a Najeriya.
Yace Kasar Saudi Arabia ta kara jarin da take dashi a bangaren kiwon dabboni a kanfanin Olam da dala Biliyan $1.2
Ya kara da cewa kuma a yanzu ana rani ne, zasu tabbatar an samu girbin Amfanin gona dan farashin kayan abinci ya fadi.