
Mata a birnin Legas sun yi barazanar yin zanga-zangar tsirara dan tursasa daina rushe musu gidaje.
Matan daga yankin Ilaje sun yi zanga-zangar lumana zuwa majalisar dokokin jihar ta Legas inda suka nemi taimakon gwamnan jihar, Babajide Sonwo Olu da kakakin majalisar Dokokin jihar,Mudashiru Obasa su saka baki a daina rushe musu gidaje.
Sun zargi sarakunan gargajiyarsu da yi musu kwacen gidaje.
Daya daga cikin matan wadda dattijuwa ce, ta fito inda take barazanar cewa, zasu yi zanga-zanga tsirara idan ba a daina rushe musu gidaje ba.
Shima shugaban mazauna yankin na Ilaje, Rafael Irowainu ya bayyana cewa wasu sarakuna na amfani da sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna rushe gidaje dan su yi gine-gine.
Ya kara da cewa, amma basu yadda shugaba ne ya aika mutanen ba.