
Kasar Iran ta bayyana cewa, zata wallafawa Duniya bayanan sirrin da ta samo daga kasar Israyla ta hanyar kutsen data mata.
Kasar Iran tace ta samu bayanan sirri ciki hadda na makaman kare dangi na kasar Israela bayan data biya wasu ‘yan kasar makudan kudade suka samo mata bayanan.
Kasar Israyla a baya itama ta yiwa kasar Iran irin wannan kutse daga baya ta kuma wallafawa kowa Duniya ta gani.
Dan haka a yanzu zamu iya cewa, kasar Iran ramako ne kate yi.