Friday, December 5
Shadow

Zan iya mùtùwà a kan APC, in ji tsohon Gwamnan Abia, Uzor Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya sake jaddada cewa a shirye ya ke ya ba da ransa akan jam’iyyar APC, musamman a jihar Abia.

Ya bayyana haka ne a hirarsa da manema labarai a garinsu na Igbere, Jihar Abia.

Da aka tambaye shi ko APC na da wata dama ta kayar da jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2027 a jihar Abia, Kalu wanda ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya ce shi da sauran magoya bayan APC za su yi aiki tukuru domin nasarar shugaban kasa a jihar.

Ya ce; “APC na da karfi a Abia. Kamar yadda na fada a wata hira, wla shirye nake in ba da raina saboda jam’iyyar. Ni mamba ne na APC kuma mai tsayawa kan gaskiyar jam’iyyar. Ni cikakken dan APC ne. Shi ya sa APC ke da karfi a Abia ta Arewa.

Karanta Wannan  Jihar Jigawa ta dakatar da Albashin malaman makarantar Firamare 239 da aka samu basa zuwa aiki, ciki hadda wanda ya shekara 3 bai je wajan aikin ba

“Jam’iyyarmu za ta yi aiki tukuru domin ganin shugaban kasa ya yi nasara a jihar. Mun taba yin hakan a baya, kuma za mu sake yin hakan a shekarar 2027.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *