Friday, December 5
Shadow

Zan Iya Shiga Mummunan Yanayi Idan Dangote Bai Aure Ni Ba, Saboda Tsananin Son Da Nake Yi Masa, Cewat Aishatu Haruna

Zan Iya Shiga Mummunan Yanayi Idan Dangote Bai Aure Ni Ba, Saboda Tsananin Son Da Nake Yi Masa, Cewat Aishatu Haruna.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

….har ta buga katin aurenta da shi

Wata ’yar siyasa a jihar Bauchi mai suna Aishatu Haruna, ta ce ta shafe shekaru shida tana dakon soyayyar attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote a ranta, inda ta ce za ta iya shiga mummunan hali idan bai aure ta ba.

Ta ce sau uku tana yin mafarkin ta aure shi, kuma ba ta jin za ta iya auren wani ba shi ba a duniya.

A cikin wata tattaunawarta da gidan rediyon Albarka da ke jihar Bauchi, Aishatu, wacce aka fi sani da Gimbiyar Mawakan Bauchi, ta kuma ce sau uku tana zuwa kamfanin attajijin na Obajana, ko za ta hadu da shi a can.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba sai idan ya yadda ya fara zama mataimakin shugaban kasa>>inji Fasto Ayodele

Aishatu wacce a 2019 ta yi takarar neman zama Majalisar Jiha dai ta wallafa hotonta ne dauke da katin gayyatar daurin aurenta da attajirin a shafukan sada zumunta, inda ta ce tana ganin ta wannan hanyar ce sakonta zai isa gare shi.

A cewarta, “Ita soyayya a zuci take, kuma ni na gamsu shi nake so, saboda yadda yake amfani da dukiyar da Allah ya ba shi wajen hidimta wa al’umma ba iya Najeriya ba, har ma da Afirka.

“Kusan shekara shida ke nan da farawar abin. Akwai lokacin ma da na yi tattaki na tafi har kamfaninsa na siminta da ke Obajana a jihar Kogi da nufin na gan shi har sau uku, amma bai yiwu ba.

Karanta Wannan  CSPR coin zasu raba $10,000 duba yanda zaku samu

“Dalilin da ya sa na buga katin shi ne saboda na san nan ce hanya mafi sauri da zai san da ni, kuma na san babu abin da ya gagari Allah,” in ji ta.

Sai dai ta tsaya kai da fata cewa ba don dukiyarsa take son shi ba, kawai ji ta yi shi kadai ne ya kwanta mata a ransa.

“Babu wanda aka haifa da dukiya, kuma ba don ita nake son shi ba, don haka ba maganar kwarya ta bi karya don baa bin da ya gagari Allah. Ni kawai yana burge ni ne,” in ji ta.

Ta ce ta gaji da dakon soyayyar a zuciyarta, shi ya sa yanzu ta fito da ita a shafukan sada zumuntar domin kada ta shiga wani halin.

Karanta Wannan  Shin matakan tsuke bakin aljihun CBN na tasiri wajen rage hauhawar farashin kaya a Najeriya?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *