Friday, December 5
Shadow

Fasto Adeboye ya bayyana ranar da zai koma ga Allah

Babban Faston Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya sake bayyana hasashe kan yadda zai rabu da duniya.

Ya ce zai mutu cikin lumana, a ranar Lahadi, bayan ya halarci cocin kuma ya ci sakwara, abincin da yafi so.

Da ya ke jawabi a rana ta huɗu na babban taron cocin na kasa da kasa mai taken “The Overcomers”, Fasto Adeboye ya jaddada cewa mutuwa ba sai da ciwo ba.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Faston ya taba bayyana wannan hasashen shekaru biyu da suka gabata, inda ya ce: “Zan mutu ne a ranar Lahadi, bayan na halarci coci, na ci sakwara da nake so, sannan in rabu da duniya ba tare da wani ciwo ba.”

Karanta Wannan  Matashiya ta Kàshè kanta saboda bata ci maki me yawa a jarabawar JAMB ba

Faston ya ce mutuwarsa za ta kasance ta gaggawa kuma salin-alin zai mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *