Wednesday, January 15
Shadow

Zanga-zanga: An saki Turawan da ake zargi da hannu a ɗaga tutar Rasha a Najeriya

An saki ɗalibai da malamai ƴan asalin ƙasar Poland da aka kama a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Poland ya bayyana a ranar Laraba.

Mutum bakwan sun shiga hannu ne a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, “bisa zargin su da hannu a ɗaga tutocin Rasha da ma ita kanta zanga-zangar,” kamar yadda jami’an tsaron Najeriya suka bayyana.

Sai dai hukumomi a ƙasar Poland sun ce waɗanda aka kama ɗin ɗalibai ne na Jami’ar Warsaw da malaminsu, waɗanda “tsautsayi ya kai su inda bai dace ba.”

Ministan Harkokin Wajen Poland, Radoslaw Sikorski ya ce yanzu an sako ɗaliban.

Karanta Wannan  ILMI KOGI: Nan Gaba Mutane Za Su Iýà Bacewa Kamar Àĺjàñù, Inji Shêikh Imam Habibi

“Ina tabbatar da cewa an sako mutanenmu ɗin nan, yanzu haka sun koma Kano sun ci gaba da karatunsu,” kamar yadda Sikorski ya wallafa wani bidiyo a shafi X.

Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa za su koma ƙasarsu ta Poland bayan sun kammala karatunsu.

A farkon watan Agusta ne aka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a Najeriya, lamarin da ya janyo tashin hankula tare da cece-ku-ce a ƙasar.

Rikicin da aka samu a wasu jihohi ya yi sanadin rasa rayuka, lamarin da ya kai ga sanya dokar hana fita.

Wani abu da ya janyo hankali shi ne yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka riƙa ɗaga tutocin Rasha, abin da ya sa jami’an tsaro suka kama mutane da dama.

Karanta Wannan  TIRƘASHI: Na Tsani Katsalaɲdan A Rayuwata, Døn Haka Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Buɗe Gashin Kaina, Saboda Ni Yin Magana Ne Ma Ke Sa Na Yi Abu, Koda Abinda Na Yi Ba Mai Kyau Ba Ne, Muddin Za A Ce Na Daina Ni Kuma A Wannan Lokacin Ne Ma Zan Fara, Inji Jarumar Finafainan Hausa, Nafisat Abdullahi

Tasirin Rasha na ƙaruwa a yankin yammacin nahiyar Afirka tun bayan juyin mulki da aka samu a ƙasashen Nijar, Burkina Faso da Mali.

Ƙasashen waɗanda yanzu ke ƙarƙashin mulkin sojoji sun fice daga ƙungiyar yankin ta Ecowas, suka kori sojojin Amurka da Faransa da yanke hulɗar dangantaka da ƙasashen Yamma sannan sun kuma suka mayar da hankali wajen ƙarfafa alaƙarsu da ƙasar Rasha.

Mahukuntan Najeriya dai sun bayyana ɗaga duk wata tuta a ƙasar baya ga ta Najeriyar a matsayin laifin cin amanar ƙasa, wanda ɗaya ne daga cikin laifuka mafi girma a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *