Saturday, May 31
Shadow

Ɓarawo ba ya zama a gwamnatin mu – Abba Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin sa ba wajen zaman ɓarayi ba ce sabo da jajircewa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Da ya ke jawabi a wajen taro da kansilolin mazaɓu 484 da ke gudana yanzu haka a gidan gwamnati, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin sa ba za ta lamunci satar kudin al’umma ba.

A cewar sa, ya na jagorantar gwamnati mai tsafta da kaffa-kaffa wajen sace kudin al’umma, inda ya jaddada cewa “ɓarawo ba ya zama a gwamnatin mu,”

Ya ce wannan kokarin yaki da din hanci ne ya sanya gwamnatin ke samun makudan kuɗaɗen da ta ke ta bijiro da aiyuka domin jin dadin al’ummar Kano.

Karanta Wannan  Daga Karshe Fasihin Yaron Nan Khalipha Aminu Ya Gana da Farfesa Isa Ali Pantami

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Gwamna Yusuf ya fadi hakan ne bayan da a kwanan nan tsohon sakataren gwamnatin, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya ke zargin badakala da wawure kuɗaɗen al’umma da gwamnatin ke yi.

A zarge-zargen sa da kafofin watsa labarai su ka yada, Bichi ya yi zargin cewa an cire shi daga sakataren gwamnatin ne saboda ya ki amincewa da a rika” kwashe Naira biliyan 2 ana sakawa a asusun tsohon gwamnan jihar kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *