Saturday, January 4
Shadow

Ƙudurin dokar haraji zai ƙara jefa jama’armu cikin talauci – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hamayyarta ga ƙudirin dokar harajin da yanzu haka ke gaban majalisar dokokin Najeriya wanda shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ne ya bayyana haka a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 a dandalin Ma’ahaha da ke birnin Kano.

Wata sanarwa da ke ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba ta ce gwamnan ya ce “wannan kundin dokar harajin ba za ta magance matsalar tattalin arziƙinmu ba. Kano tana hamayya da wannan ƙudiri da zai shafi walwalaw al’umma.”

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tankiyya tsakaninta da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda ya soki kundin.

Karanta Wannan  Kalli Hoton Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Atiku Abubakar da Peter Obi da ya dauki hankula

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *