Monday, December 16
Shadow

Ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya ta bi sahun yajin aikin ƙwadago

Ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya ta umarci mambobinta da su shiga yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar NLC da TUC suka shiga a kan dambarwar mafi ƙanƙantar albashi a ƙasar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babban Sakatarenta, Achike Chude, a jiya Lahadi, ƙungiyar ta umarci dukkanin shugabanninta a matakai daban-daban a jihohin ƙasar har da Abuja su tabbatar ƙungiyar ta shiga yajin aikin, domin mara baya ga manyan ƙungiyoyin ƙwadagon.

Sanarwar ta ce matakin ya zama wajibi saboda gazawar gwamnati kan yarda da buƙatar samar da albashin da ma’aikatan Najeriya za su iya rayuwa da shi.

Rahotanni na nuna cewa yajin aikin na gama-gari da manyan ƙungiyoyin ƙwadagon na Najeriya suka shiga daga yau Litinin na samun karɓuwa a fadin ƙasar, yayin da shugabannin ƙwadago ke bi ma’aikatu da sauran wuraren aiki a jihohi har ma da Abuja babban birnin ƙasar domin tabbatar da ma’aikata sun ƙaurace wa wuraren aikin.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kungiyar kwadago ta NLC ta kulle tashar wutar Lantarki ta Najeriya inda hakan ya jefa kasar cikin Duhu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *