Ƴan Majalisar Wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga PDP zuwa APC

Ƴan majalisar wakilai 6 daga jihar Delta sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ne ya bayyana haka a zaman majalisar na yau Talata bayan ta dawo daga hutu.
Yan majalisa shidan da su ka sauya sheka daga PDP zuwa APC sun hada da Victor Nwokolo; Dan majalisa Julius Pondi; Dan majalisa Thomas Ereyitomi; Nicholas Mutu; Okodiko Jonathan da kuma Nnamdi Ezechi.
Wasu ‘yan jam’iyyar Labour ma guda biyu daga jihar Enugu su ma sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, waɗanda su ka hada da Mark Obetta da Dennis Nnamdi.
Shugaban majalisar ya ambato ‘yan majalisar na cewa sun sauya sheka ne sakamakon rikicin da ya barke a jam’iyyunsu a jihohinsu da kuma a matakin kasa.