
A ranar Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Sifaniya, Real Madrid da Barcelona za su ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey.
Wasan wanda ake yi wa laƙabi da el-classico – na ɗaya daga cikin wasannin da suka fi jan hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.
Ƙungiyoyin sun kawo wannan matakin ne bayan da Real ta doke Real Sociedad da ci 5-4 a wasa gida da waje.
Ita ma Barcelona ta kawo matakin ne bayan fitar da Atletico Madrid da ci 5-4 gida da waje.
Barcelona ce ƙungiyar da ta fi ɗaukar kofin na Copa del Rey a tarihi, bayan da ta ɗauki kofin har sau 31, yayin Real Madrid ta ɗauki kofin sau 20.
A yanzu haka Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 76, yayin Real Madrid ke matsayi na biyu da maki 72, inda ya rage wasa biyar a ƙarƙare gasar ta bana.
Wasu fitattun ƴan wasan ƙungiyoyin na fama da jinya ciki har da Robert Lewandowski da Eduardo Camavinga, don haka ba za su buga fafatawar ba.