
Wasu mahara da ake zargin ƴanbindiga ne masu ikirarin jihadi sun kashe sojoji takwas a arewacin ƙasar Benin, kamar yadda majiyar tsaro ta shaida wa AFP a ranar Juma’a.
Harin ya auku ne a sansanonin sojojin ƙasar guda biyu a ranar Alhamis, sai dai majiyar ta ƙara da cewa an kashe maharan guda 11 a gwabzawar.
Waɗanda suka jikkata yanzu suna kwance suna jinya a wani asibiti a ƙasar.
Sojojin Benin dai suna cigaba da gwabza yaƙi a yankin ne domin fatattakar ƴanbindiga, inda ko a Janairun 2022 ta aika ƙarin sojoji 3,000.
Ko a watan Janairun da ya gabata an kashe sojojin Benin 29 a wani hari da ƙungiyar GSIM mai alaƙa da Al Qaeda ta ɗauki alhaki.