Thursday, January 9
Shadow

Ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a Zamfara

Rahotanni na cewa ana ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan sauƙin da aka samu a ƴan watannin nan.

Wasu mahara sun shiga garuruwa da dama na ƙaramar hukumar Maru, inda suka kashe aƙalla mutum 20 tare da yin garkuwa da gommai.

Waɗanda BBC ta zanta da su sun ce ƴan bindigar sun shiga garuruwan ne da motoci inda suka kwashi kayan abinci da sauransu.

Wannan dai na zuwa ne bayan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu na hallaka wasu daga cikin shugabannin ƴan bindigar a jihar ta Zamfara.

Karanta Wannan  Kalli yanda aka ga wani katon Kunkuru yana yawo a Maiduguri bayan Ambaliya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *