
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed kan zargin kashe kishiyar mai suna Hajara Isa hanyar shaƙeta a gidan mijinsu.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, Ahmed Wakil ya fitar ranar Talata ya ce tuni rundunarsu ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Ya ce mijin matan – Sale Isa – ne ya kai ƙorafi wajen ƴansanda a ranar Talata.
Wakil ya ce bayan fara gudanar da bincike ƴansanda suka kama matar mai suna Fatima Mohammed mai shekara 28, wadda daga baya ta amsa laifinta a lokacin ƴansanda suke tuhumarta.
“A lokacin da ake tuhumarta ta amsa laifinta inda tace shaƙe kishiyartata ta yi, har sai da ta mutu”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ”bayan ta kashe ta, ta yi ƙoƙarin yin ɓadda-bami, ta yadda ba za a zarfgeta ba, inda ta watsa mata ruwan zafi, sanna ta ƙonata da wasu buhun da ya fara lalacewa”.
Tuni dai aka mayar da binciken ofishin kula da manyan laifuka da ke jihar domin faɗaɗa bincike.
A baya-bayan nan jihar Bauchi na fuskantar matsalolin kisan kai, wani da ke ƙara haifar da fargaba.
A farkon makon nan ma an kama wani matash bisa zargin kashe mahaifiyarsa, bayan da a farkon azumi aka zargi wani miji da kashe matarsa.