Friday, December 5
Shadow

Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo

Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo.

Ɗan Majalisar Wakilai, mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Fagge, Muhammad Bello Shehu, ya sayi wa injin faci ga wani tsoho da ke buƙatar injin.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne faifen bidiyon tsohon, mai suna Ali Abdulrahman, wanda aka fi sani da Ali Mai Faransawa, ya karade kafafen sadarwa, inda ya ke korafin cewa ya shafe shekaru ya na tafiyar Kwankwasiyya amma bai taɓa samun wani tagomashi ba.

A cewar Ali Mai Faransawa, wani kansila a Fagge ya yi masa alƙawarin haɗa shi da shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge domin a saya masa injin faci, amma abun ya ci tura.

Karanta Wannan  Hukumar JAMB ta fitar da Jadawalin Jihohin da aka fi yin satar amsa, Duba kaga ko jiharka na ciki

Bidiyon ta sa, wacce gidan rediyon Express FM ya wallafa a shafin sa na facebook, ta daukin hankalin yan Kwankwasiyya, inda har wasu manyan ciki su ka yi alƙawarin share hawayen wannan tsoho, mai kimanin shekaru sama da 70.

Da ya ke zantawa da wakilin DAILY NIGERIAN HAUSA, Ali Mai Faransawa, wanda ɗan asalin unguwar Fagge D2 ne, ya ce ya na zaune ya ga hadiman dan majalisar sun zo sun ce ya taso a je a saya masa injin da ya ke buƙata.

A cewar Mai Faransawa, wanda ke sana’ar faci a kasuwar Wambai, ya ji matuƙar farin ciki da ya ji an zo za a share masa hawaye, inda ya kara da cewa ya dade ya na neman ya sayi wani injin tun bayan lalacewar nasa, lamarin da ya durkusar da san’ar ta sa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka baiwa Hamata Iska a wajan taron masu ruwa da tsaki na a Arewa Maso saboda ance sai Tinubu ba'a hada da sunan Kashim Shettima ba

Ya godewa Muhammad Bello Shehu, da aka fi sani da MB Shehu, inda ya yi addu’ar Allah Ya sa ya yi ta yin ɗan majalisa.

“Na yi farin ciki matuƙa. Ban san da me zan saka wannan alheri ba, sai dai kawai na yi addu’ar samun nasara ga MB Shehu.

“Allah Ya bashi nasara a duk lokacin zaɓe. Allah Ya jikan mahaifan sa, Ya inganta iyalin da, Allah Ya Yi riko da hannun sa.

“Ina yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf godiya da su ka tayar mana da wannan jajirtaccen wakili mai tausayin talakawa. Nagode kwarai,” in ji Ali Mai Faransawa.

Karanta Wannan  Bincike: Karanta Jadawalin jihohin da aka fi samun matan aure na aikata Zìnà, 'yan mata ma na lalata, Rahoton yace babu irin wadannan matan ko daya a jihohin Jigawa, Katsina da Kebbi sannan Kuma jihar Taraba ce ta daya a Arewa wajan aikata wannan masha'a

Ya kuma baiyana cewa wannan inji da aka sai masa zai farfaɗo da sana’ar sa, ya ci gaba da ɗaukar dawainiyar iyalin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *