Thursday, May 22
Shadow

Zulum zai mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 gidajensu saboda ‘ƙaruwar karuwanci’ a sansanoni

Gwamnan jihar Borno a arewacin Najeriya ya bayyana shirinsa na mayar da iyalai 6,000 da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu sakamakon abin da ya bayyana da “ƙaruwar karuwanci” a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Yawancin mutanen sun ftio ne daga ƙananan hukumomin Dikwa da Mafa, kamar yadda Gwamna Babagana Zlumu ya bayyana a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri.

A cewarsa, dole ne mutane su koma gidajensu domin su ci gaba da neman abin dogaro da kansu.

“Mun lura cewa a sansanin ‘yan gudun hijira akwai ƙaruwar karuwanci, da yawaitar ‘yandaba, da cin zarafin yara, da kuma aikata laifuka iri-iri,” in ji shi cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar.

Karanta Wannan  El-Rufai, Amaechi,Buhari, da Osinbajo basu je taron masu ruwa da tsaki na APC ba

Ya kara da cewa tuni aka mayar da kashi 75 cikin 100 na mazauna sansanin gidajensu.

Gwamnan ya kuma ce kowane magidanci zai samu tallafin naira 100,000, yayin da matarsa za ta karɓi 50,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *