Tsagin NNPP ya caccaki Kwankwaso bisa sukar waɗanda su ka bar jam’iyyar zuwa APC a Kano.

Wani tsagi na jam’iyyar NNPP, ya caccaki Sanata Rabi’u Kwankwaso kan yadda ya bayyana ‘ya’yan kungiyar Kwankwasiyya da suka koma APC a matsayin maciya amana, inda ta ce Kwankwaso ne maciya amana.
A tuna cewa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa, ya caccaki wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP a jihar Kano, wadanda kwanan nan suka sauya sheka zuwa APC, inda ya bayyana abin da suka yi a matsayin cin amana.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a gidansa da ke Miller Road da ke Kano a yammacin ranar Juma’a, a lokacin da wasu ’yan kungiyar kwankwasiyya daga karamar hukumar Takai suka ziyarce shi.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Legas, Shugaban NNPP na kasa, Dr Agbo Major ya ce Kwankwaso ba shi da ikon yin magana a madadin jam’iyyar.
“An kori Sanata Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP tare da mabiyansa karkashin jagorancin Dr Ahmed Ajuji.”
A cewar Major, Kwankwasiyya ba jam’iyyar siyasa ba ce, kungiya ce da ta shiga jam’iyyar NNPP bayan zaben shugaban kasa na 2023 inda shugabansu ya zama mai rike da tutar jam’iyyar.