Friday, December 5
Shadow

2027: Da yiwuwar Kwankwaso ya shiga APC – Kofa

Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bai rufe kofar shiga jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen 2027.

Jibrin, jigo a jam’iyyar NNPP, ya ce Kwankwaso har yanzu ya bar kofar tattaunawa a bude da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, duk da kasancewarsa ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.

Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels inda ya ƙara da cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ƙarfin siyasa ce da ba za a iya watsi da ita ba.

Sai dai ya nuna yiwuwar wasu masu ruwa da tsaki a APC na Kano na iya hana shigar Kwankwaso saboda muradunsu na siyasa.

Karanta Wannan  Al'ummar Kano Sun Zargi 'Yansanda Da Yunƙurin Sanya Dokar Ta-baci Kan Gayyatar Sarki Sunusi

Jibrin, wanda ya sha ganawa da Shugaba Tinubu, ya ce komai yana yiwuwa a siyasa, duk da kasancewarsa ɗan Kwankwasiyya.

A zaɓen 2023, Kwankwaso ya samu kuri’u sama da miliyan ɗaya da ɗari huɗu, inda ya zo na huɗu, yayin da Tinubu ya lashe zaɓen da kusan kuri’u miliyan tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *