Friday, December 5
Shadow

Tinubu ya jajanta wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar jami’in sojan ƙasar Birgediya Janar Musa Uba, wanda mayaƙan ƙungiyar Iswap suka kashe a jihar Borno.

An fara fargabar mutuwar Janar Uba ne bayan ƙungiyar ta yi iƙirarin kashe shi, da kuma fitar da wani bidiyo.

Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta ce a ƙarshen makon da ya gabata ne ‘yanbindigar suka yi wa dakarunta kwanton ɓauna, waɗanda janar ɗin ke jagoranta.

Zuwa yanzu rundunar ba ta ce komai ba game da bidiyon da ke yawo a intanet.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce mutuwar janar ɗin “ta kaɗa” shi.

Karanta Wannan  Karka Dauka Adawace: Da gaske ana wahala a Najeriya>>Atiku ya gayawa Tinubu

“A matsayina na babban kwamandan tsaro na ƙasa, na ji takaici da mutuwar sojojinmu a bakin aiki. Allah ya bai wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba da sauran dakaru haƙuri,” in ji shugaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *