Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun kashe Naira Biliyan 8.64 wajan tafiye-tafiye a cikin watanni 3 kacal da suka gabata.
An gano hakanne ta hanyar Amfani da wata manhaja me suna Govspend da ake amfani da ita wajan bibiyar kudaden da gwamnati ke kashewa.
Hakanan an gano cewa an kashe Naira Biliyan 12.59 wajan kula da jiragen da suka yi amfani dasu wajan yin wadannan tafiye-tafiye.