Monday, December 16
Shadow

Tsagaita wuta a Gaza: Ministocin Isra’ila sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin Netanyahu

Wasu Ministocin Isra’ila biyu masu tsatsauran ra’ayi sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin hadin gwiwar ƙasar idan har Benjamin Netanyahu ya amince da tayin sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da shugaba Biden na Amurka ya gabatar.

Yarjejeniyar da Mista Biden ya sanar ta samu karɓuwa daga ɓangaren ƴan adawa a Isra’ila da ƙasashe masu shiga tsakani.

A ranar juma’a ne shugaba Biden ya yi tayin tsagaiwa wutar ta hanyar bullo da matakai uku, da suka haɗa da tsagaita wuta na mako shida a matakin farko.

Tare da janyewar dakarun Isra’ila daga wurare masu yawan jama’a a Gaza.

Sannan ya ce yarjejeniya za ta bayar da damar sakin Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na dindin tare da sake gina Gaza.

Karanta Wannan  Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza - Biden

To sai dai ministan tsaron Isra’ila Itamar Ben-Gvir, ya ce duk wata yarjejeniya da za ta haifar da tsagaita wuta kafin a ruguza Hamas, to wata nasara ce ga ta’addanci.

Yayin da shi ma a nasa ɓangare Ministan kudi, Bezalel Smotrich, ya ce yana adawa da duk wani matakin sasantawa Muddin ba a kawar da Hamas ba.

To sai dai ɗaya daga cikin ‘yan siyasar hamayya masu ƙarfin faɗa a ji, Yair Lapid ya yi tayin mara wa Natanyahu baya idan ya amince da yarjejeniyar.

A ɗaya ɓangaren kuma dubban Isra’ilawa da ke zanga-zanga a Tel Aviv sun buƙaci gwamnatin ta amince da yarjejeniyar ta shugaba Biden.

Karanta Wannan  Kasar Maldives ta haramtawa Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan Falasdinawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *