
Mutane huɗu sun ƙone ƙurmus wasu goma kuma sun ji raunuka yayin da wata mota ƙirar bas (Hummer) ta kama da wuta a garin Gwaram da ke jihar Jigawa.
Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma, a jiya Asabar a kusa da makarantar sakanadare ta haɗaka ta gwamnati ta ‘yammata da ke garin na Gwaram (Government Girls Unity Secondary School )
Wata sanarwa da kakakin ‘yansanda na jihar SP Lawan Adam ya fitar a yau Lahadi ta nuna cewa motar ta tashi ne daga ƙaramar hukumar Zaki ta jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.
Sanarwar ta ce, ”motar na ɗauke ne da fasinja 44, da suka haɗa da manya 25 da yara 19.”
Kakakin ‘yansandan ya ce, wutar ta kama ne sakamakon katifa da aka ɗaure a bayan motar da ke kusa da salansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa mutum goma da suka ji rauni an kai su asibitin Gwaram yayin da sauran aka yi nasarar tserar da su daga motar ba tare da wani rauni ba.
Waɗanda suka rasun kamar yadda sanarwar ‘yansandan ta nuna su ne Zuwairah Hassan, mai shekara 40 da Fatima Hassan, mai shekara 5 da Iyatale Hassan mai shekara 3 da Halima Muhammad mai shekara 10, dukkanninsu daga ƙauyen Saldiga da ke yankin ƙaramar hukumar Zaki.