
Rahotanni daga jihar Delta sun bayyana cewa, wasu mahara sun shiga coci a garin Asagba Ogwashi dake karamar hukumar, Aniocha South ta jihar ina suka harbi fasto suka sace mutane 6.
Kakakin ‘yansandan jihar, Mr. Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace tuni jami’ansu suka bazama daji dan bin sahun masu garkuwa da mutanen.
Zuwa yanzu dai maharan basu kira ‘yan uwan wadanda suka sace din ba.
Tuni aka garzaya da faston zuwa Asibiti dan duba lafiyarsa.