
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya taya al’umma musulmi murnar fara azumin watan Ramadan na shekarar 2025, inda ya yi addu’ar Allah ya sa azumin ya zo da albarka.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani saƙo ya fitar, inda a ciki ya ce kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu game da manufufin gwamnatinsa.
Ya ce, “muna godiya ga Allah da ya nuna mana farkon wannan azumin lafiya, wanda ya zo a daidai lokacin da muke ƙokarin inganta ƙasarmu. A game da manufofin da muka ɗauka masu tsauri, kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu domin tattalin arzikin ƙasarmu ya fara inganta.
“Haka kuma farashin abinci, wanda a baya ya yi tashin gwauron zabi, yanzu ya fara sauka, wanda hakan sauƙi ne ga masu azumi da ma sauran ƴan Najeriya baki ɗaya. Naira na ƙara samun daraja, sannan farashin man fetur na raguwa. Duk waɗannan abubuwan suna nuna cewa akwai haske ne a gaba,” in ji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga musulmi da su yi amfani da watan wajen ƙara imani da tausayin juna da kuma yin addu’a domin ci gaban ƙasa.