Friday, December 5
Shadow

An yankewa malamin jami’a hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da yiwa dalibarsa Fyàdè

Wata kotun musamman dake kula da rikice-rikicen cikin gida dake Ikeja jihar Legas ta yankewa wani malami a kwalejin ilimi ta Adeniran Ogunsanya College of Educatio daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa dalibarsa fyade.

Malamin me suna Kolawole Muyiwa ya musanta zargin da ake masa bayan da aka gurfanar dashi a gaban kotun.

Ya aikata laifinne a ranar 11 ga wata October na shekarar 2021 a farfajiyar makarantar.

An gabatar da shaidu da suka hada ‘yansandan da suka yi bincike akan lamarin, da lauya da wadda akawa fyaden.

Mai shari’a, Justice Rahman Oshodi ya bayyana cewa, duka wadanda suka bayar da shaida akan lamarin labarinsu yayi daidai da wadda akawa fyaden dan haka aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Shinkafar da aka bamu bata dahu ba, kuma ba nama, Inji daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *