Ministan kudi Wale Edun ya bayyana cewa duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama dashi, ana tsammanin nan gaba kadan matsalar zata ragu.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV a jiya Lahadi.
Yace gwamnatin Tinubu ta dauki matakai na magance matsalar kuma tattalin arzikin kasarnan na tafiya ta hanyar dake nuna ci gaba.
Ya bayar da tabbacin cewa, cikin ‘yan watanni masu zuwa za’a ga canji da ci gaba ta fannin tattalin arzikin