Sunday, March 16
Shadow

An yiwa wannan faston daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa yarinya me shekaru 13 fyàdè

Kotu dake za zama a jihar Ekiti a ranar Litinin dinnan ta daure wani Fasto me sunan Adeleye Akingbaso da shekaru 47 bisa laifin yiwa yarinya me shekaru 13 fyade.

Wanda ake zargi din abokin mahaifiyar yarinyar da yawa fyadene.

da take bayar da labarin yanda lamarin ya faru tace Adeleye yakan kwana a gidansu, tace ranar da abin zai faru mahaifiyarta tana aikin dare ne.

Tace tana kwance ya tashe ta yace wai ta yi fitsarin kwance tace abin ya bata mamaki, nan dai ya ciro wani mai ya shafa mata a gabanta.

Tace daga nan bata san abinda ya faru ba da ta tashi ta ga an yi mata fyade tace ya gargade ta da cewa idan ta fada zai kasheta.

Karanta Wannan  Hotuna:Kalli Yanda aka gano wasu matsafa dake kwakule Kaburbura suna sace sassan jikin mutane a jihar Borno

Tace a rana ta biyu ya isketa a dakin dafa abinci shima mahaifiyarta bata nan inda yace mata yana son kammala abinda ya fara saidai anan ta ki yadda inda ta yi ihu makwabta suka taru.

Tace an kira mahaifiyarta aka sanar da ita inda aka gayawa ‘yansanda.

Me gabatar da kara, Taiwo Ariyo ya kira shaidu 4 da gabatar da takardar Asibiti data tabbatar da an wa yarinyar fyade.

Me shari’a Justice Blessing Ajileye tace an samu wanda ake zargi da laifi inda ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan gyaran hali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *