Kungiyar dalibai ta kasa NANS zata yi zanga-zangar kalubalantar rufe Makarantun Boko a wasu jihohin arewa saboda Azumin Ramadan.

Kungiyar tace zata yi zanga-zangar ce in har jihohin Kano, Bauchi da Kebbi da Katsina basu janye umarnin rufe Makarantun da suka yi ba.
Itama kungiyar Kristocin Najeriya ta kalubalanci rufe Makarantun.
Wadannan jihohi sun bayar da hutun ne don saukakawa al’umma musamman Malamai wahalhalun Azumin.