
Majalisar dattijai ta bayyana cewa, Sanata Natasha Akpoti ta zargi kakakin majalisar da neman yin lalata da itane kawai dan ta dauki hankulan nmutane.
Kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana haka a hirar da kafar ChannelsTV ta yi dashi.
Yace har kofar majalisa Sanata Natasha Akpoti ta je ta yi kiss ita da mijinta.
Yace ba yace hakan ya sabawa doka bane amma ai ana barin halas dan kunya dan kuwa hakan ya sabawa al’ada da dabi’ar mutanen kasarnan.
_Yace Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata ne kawai dan ta dauki hankalin mutane.