
‘Yan kasuwar man fetur din Najeriya sun sha Alwashin kawo man fetur din da ya fi na Dangote sauki daga kasashen waje.
A matatar man Dangote, yana baiwa ‘yan kasuwar man a kan farashin sari na Naira 825 kan kowace lita.
Saidai ‘yan kasuwar sun ce farashin sari da suke siyo man fetur din daga kasashen waje ya fadi zuwa Naira 774.72 akan kowace lita wanda hakan yasa ake sayar da man fetur din akan farashin Naira 800 a gidajen man fetur.
‘Yan kasuwar sun ce farashin sari na Naira 774.72 da suke saro man fetur din daga kasashen waje ya nuna ana samun saukin Naira 50.28 akan kowace lita idan aka kwatanta da farashin sari da Dangote ke basu man fetur din.
Wannan sauki da ake samu ne yasa da yawan ‘yan kasuwar ke son daina siyan man a hannun Dangote inda suke son komawa siyowa daga kasashen waje.