Friday, March 14
Shadow

Zargin Da Natasha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio cikin cokaline, An gano munanan abubuwan da ake zargin Sanata Akpabio da aikatawa wanda suka dame zargin da Natasha ke masa

Kafar Gistlover da aka sani da yiwa shahararrun mutane Tonon silili ta bankado munanan ayyukan da ake zargin Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da aikatawa.

Kafar tace tana da takardu da shaidar duk zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio.

Da farko dai tace Zargin da Sanata Natasha Akpoti kewa Akpabio cikin cokaline idan aka kwatanta abinda ake zarginsa dashi.

Kafar tace Sanata Akpabio lokacin yana Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya rika yin lalata da kwamishinoninsa, ciki hadda matan aure.

Sannan yakan rikewa dan kwangila kudi ko takardu yace sai ya kai masa matarsa yayi lalata da ita.

Hakanan Matarsa, ‘ya’ya 4 mata ta haifa inda take neman da Namiji ido rufe, dalilin hakane yasa aka boyeta a kasar Amurka na tsawon watanni 9, aka siyo jariri daga gidan da ake haihuwar jarirai irin na inyamurannan aka bata ta dawo dashi Najeriya da sunan cewa danta ne.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ina masu neman tafsirin malam Attalili Attagazuti, to gashi

Wadda ta haifi jaririn daga baya ta gano cewa Akpabio ne ya sayi danta, sai ta nemi karin kudi, Kafar Gistlover tace dalilin hakane aka kashe matar.

Ana zarginsa da satar Naira Biliyan 205 wadanda ake zargin ya sata a yayin da yake gwamnan jihar Akwa-Ibom.

Sannan akwai zarge-zargen kashe mutane da yawa da ake masa shi da matarsa.

Kafar tace tana da takardu da shaidar duka wadannan abubuwan da suka faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *