
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan APC ne, kuma ya fi so a rinƙa alaƙanta shi da jam’iyyar.
Wannan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi da BBC ranar Alhamis inda ya ce “sai da Buhari ya amince sannan na bar jam’iyyar APC zuwa SDP.”
Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da tsohon kakakinsa, Garba Shehu ya fitar, inda ya ce ba ya so ya bar kowa a cikin ruɗani game da inda yake, domin a cewarsa ba zai taɓa juya wa jam’iyyar da ta ba shi damar tsayawa takara har ya yi shugabancin ƙasa na wa’adi biyu baya ba.
“Ni ɗan APC ne, kuma na fi so ana alaƙanta da jam’iyyar, sannan zan yi duk mai yiwuwa wajen tallata jam’iyyar.”
Buhari ya ƙara da cewa babu abin da zai ce game da jam’iyyar APC sai dai godiya bisa goyon bayan da ya samu daga jam’iyyar, a lokacin da yake mulki da bayan ya kammala wa’adinsa, wanda a cewarsa alfarma ce babba da ba zai taɓa mantawa ba
Ya kuma ce wahalar da waɗanda suka assasa jam’iyyar suka sha wajen kafa jam’iyya mai ƙarfi domin kare martabar kundin tsarin mulki da dimokuraɗiyya ba za ta tafi a banza ba.
Me El-Rufa’i ya faɗi?
Tsohon gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasir El-Rufai dai ya ce bai bar jam’iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam’iyyar APC da komawa jam’iyyar SDP.
“Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma’a na faɗa masa cewa zan bar jam’iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba.
Ko lokacin da nake gwamnan Kaduna da zan naɗa kwamishoni sai da na kai masa jerin sunayen domin ya duba ya gani ko a ciki akwai wanda ya taɓa zagin sa.
Bayan ya duba ya ce ba matsala Allah ya yi albarka. Duk abin da zan yi sai na yi shawara da shi.” In ji Malam El-Rufai.