
Wani mutum dan kimanin shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi ya mutu a dakin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin fita daga dakin.
Lamarin ya farune a sabuwar Kutunku dake Gwagwalada a baban birnin tarayya, Abuja.
Lamarin ya farune ran Asabar da misalin karfe 5 na yamma inda karuwar data ga haka ya ruga ta sanar da manajansu.
Manajan ya garzaya dakin inda ya gane mutumin me suna Ajayi Nicholas inda ya yi gaggawar sanar da ‘yan uwansa dake yankin.
An garzaya dashi Asibiti inda acan likitoci suka tabbatar da ya mutu
‘Yansanda sun je wajan inda suka gudanar da bincike kuma tuni aka kai gawar wanda ya mutun makwanci.