
Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya yabawa Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda kokarin tayar da komadar tattalin arzikin da take.
A bayanin da ya yiwa ‘yan Jarida ranar Lahadi a Kano, Tanko Yakasai ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya sun fara samun sauki daga matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.
Yace farashin kayan masarufi da na man fetur na ci gaba da sauka.
Yakasai yayi kira ga ‘Yan Arewa dama Najeriya baki daya dasu ci gaba da baiwa gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu goyon baya.
Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu na kokarin samar da ci gaban kasa kuma Arewa ba’a barta a baya ba a wannan kokari.