
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya zargi Gwamnan jihar me ci, Malam Uba Sani da yin amfani da kudaden kananan hukumomi ya sayi gidaje a kasashen Seychelles, South Africa, da the United Kingdom.
EL-RUFAI wanda bai dade da barin jam’iyyar APC zuwa SDP ba ya bayyana hakane a yayin hirar da aka yi dashi a gidan rediyon Najeriya dake Kaduna ranar Talata.
Yace gwamna Uba Sani na karkatar da kudaden kananan hukumomi inda yake canjasu zuwa dala bisa shirin sayen gidaje.
Yace amma shi a zamanin mulkinsa ba abinda yayi kenan ba.
Yace a zamaninsa suna baiwa kananan hukumomi kudadensu, yace shuwagabannin kananan hukumomi na APC da PDP duk suna nan da rai kuma zasu iya bayar da shaida akan hakan.
Yace amma hukumomin gwamnatin tarayya sun ki cewa uffan kan abinda Gwamna Uba Sani yake yi ne saboda wani ne daga sama yake bashi umarni.
El-Rufai ya kara da cewa, ana amfani da ‘yan canji ne wajan satar kudin, yace gwammatin dake zarginsu da rashawa da cin hanci gashi itama tana yi dumumu.