Monday, December 16
Shadow

Ƴan ƙwadago sun rufe hanyar shiga kamfanin man fetur na Najeriya

Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya sun rufe hanyar shiga babban ofishin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Hakan ya zo ne jim kaɗan bayan fara yajin aikin ƴan ƙwadago, wanda ƙungiyoyin NLC da TUC suka kira kasancewar an gaza cimma matsaya tsakanin ƴan ƙwadagon da gwamnati game da albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.

Yanzu haka dai ana cikin hali na rashin tabbas kan tasirin da yajin aikin zai yi, sai dai ana fargabar zai iya tsayar da al’amura a faɗin ƙasar.

Ƴan ƙwadagon na buƙatar gwamnati ta amince da naira 497,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, sai dai gwamnati ta tsaya a kan naira 60,000.

Karanta Wannan  Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *