Kasar Maldives ta hana Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan da Israela kewa Falas-dinawa.
Shugaban kasar, Mohamed Muizzu ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.
Jimullar Yahudawan Israela dubu 11 ne suka je kasar ta Maldives yawom shakatawa a shekarar data gabata.
A matsayin martani ga wannan matakin na kasar Maldives, ministan harkokin kasashen waje na Israelan Israelan Oren Marmorstein yace duk ‘yan kasarsu da suke kasar ta Maldives su fice.