Monday, May 19
Shadow

Da Duminsa: Dangote ya sake rage farashin Man fetur dinsa

Matatar Man fetur ta Dangote ta sake sanar da kara rage farashin Man fetur dinta inda a yanzu take sayarwa ga masu sari akan 835 kan kowace Lita maimakon 865 kan kowace Lita da ake sayarwa a baya.

A ranar Laraba ne dai matatar man ta sanar da abokan huldarta da rage wannan sabon farashin.

Wannan ne karo na 3 da matatar man ta Dangote ke rage farashin man ta a cikin makonni 6 da suka gabata.

Karanta Wannan  Duk da dakatar dashi da yayi, Gwamna Fubara na jihar Rivers ya gayawa al'ummar jihar su ci gaba da goyon bayan shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *