Wednesday, May 21
Shadow

Ƴànbìndìgà sun kàshè mutane biyu tare da sàcè mutum ɗaya a Kano

Wasu da ake zargin ƴan fashin jeji ne sun kai hari garin Faruruwa da ke Karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da ba a bayyana adadinsu ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a kasuwar garin da misalin karfe 7 na dare a jiya Alhamis, inda suka fara harbe-harbe kan me uwa da wabi.

Wani shaida, Ibrahim Faruruwa, ya ce maharan sun yi yunkurin sace wani hamshakin dan kasuwa, Alhaji Haruna Halilu, sai dai ba ya shagon nasa a lokacin harin.

Ya ce: “Da basu samu Alhaji Haruna ba, kawai sai suka sace dansa, Mas’ud.”

Karanta Wannan  'Yan kasuwar man fetur zasu shigo da man fetur daga kasashen waje wanda yafi na Dangote Sauki

Ya kara da cewa maharan sun kashe mutane biyu — wato Alhaji Rabiu Faruruwa da Sahabi Dankwaro a yayin harbe-harben da su ka riƙa yi.

Wani mazaunin garin, Abubakar Hamza Adam, ya ce dan uwansa karami, Zunnurain, ya samu rauni a yayin harin.

Ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. ’Yan bindiga sun kai hari a Faruruwa, Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano. Wasu mutane sun mutu, wasu kuma an sace su.

“Dan uwana Zunnurain ya ji rauni a hannunsa, sannan an kwace masa wayar salula.

“Allah ya kare rayukanmu da dukiyoyinmu, ya kuma hana faruwar hakan a gaba.”

Da Daily Nigerian ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yansandan jihar, Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya ce zai bincika lamarin sannan ya sanar da wakilin ta, amma har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto, bai dawo da bayani ba.

Karanta Wannan  Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NATCA tace aiki ya mata yawa tana fama da matsanancin karancin ma'aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *