Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ƙungiyar ƙwadago ta yi cewa sojoji sun kewaye wurin da suke tattaunawa da wakilan gwamnatin ƙasar, tana mai cewa masu ba da kariya ne ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
Ɗazun nan muka kawo muku rahoton cewa NLC ta yi zargin sojoji sun yi wa ofishin sakataren gwamnatin tarayya tsinke yayin da suke ganawa da wakilan gwamnati kan yajin aikin da suke yi.
Sai dai cikin wani martani da ta mayar a kan saƙon da NLC ta wallafa a dandalin X, rundunar sojan ta ce ba haka abin yake ba.
“Ku sani cewa Mallam Nuhu Ribadu ma yana halartar ganawar kuma ya isa wurin ne da sojoji masu gadinsa da doka tanada,” in ji saƙon.
“Da zarar ganawar ta ƙare jami’an tsaron za su fice daga wurin tare da shi.”