Friday, December 12
Shadow

Babu irin muguntar da Buhari bai shiryawa Tinubu ba dan ya fadi zaben 2023 amma da yake Allah na sonshi, ya tsallake>>Inji Ministan Abuja Wike

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa, babu irin muguntar da tsohuwar gwamnatin APC batawa Tinubu ba dan kada ya zama shugaban kasa ba amma Allah ya tsallakar dashi.

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.

Yace An kawo sabbin tsare-tsare na wahalar man fetur da canjin kudi da sauransu duk dan a hana Tinubu zama shugaban kasa amma Allah ya tsallakar dashi.

Yace haka ne ke faruwa dama idan Allah na son mutum.

Yace kuma babu maganar wani dan Arewa ya sake zama shugaban kasa a Najeriya har sai bayan shekarar 2031 bayan Tinubu ya kammala mulkinsa zango na biyu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Abin takaici ne yanda aka baiwa 'yan mata 'yan kwallon Najeriya kyautar Naira Miliyan 160, kudin da har soja ya gama aikinsa in za'a hada duka abinda zai samu ba zai kai hakan ba>>Soja ya koka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *