Tuesday, August 25
Shadow

Na yiwa Atiku Makarkashiya a zaben shekarar 2023 duk na ni dan PDP ne hakanan idan ya sake tsayawa takara a shekarar 2027 zan sake yi masa makarkashiya>>Inji Ayodele Fayose

Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayse ya bayyana cewa, a zaben shekarar 2023 ya yiwa Atiku Abubakar makarkashiya.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels.

Yace babbar matsalar da aka samu a PDP shine da aka baiwa dan Arewa damar tsayawa takarar shugaban kasa bayan da dan Arewa ya kammala shekaru 8 yana mulki.

Yace Najeriya tafi PDP muhimmanci.

Yace kuma idan Atiku ya sake cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027, zai sake yi masa makarkashiya.

Hakan ya zowa mutane da yawa da bazata musamman ganin cewa, shi Fayose dan PDP ne.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ka rika shan ruwan Alwala ko Zuciyarka ta yi sanyi>>Sheikh Salihu Zaria ya gayawa Dr. Jamil bayan ya sokeshi saboda kaiwa Dr. Junaid ziyara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *