Tuesday, May 20
Shadow

Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Jos, babban birnin jihar Filato saboda yawaitar Kàshè-Kàshè

Rahotanni daga jihar Filato na cewa, zanga-zanga ta barke a babban birnin jihar watau, Jos saboda yawaitar kashe-kashen ‘yan Asalin Jihar da ake zargin ‘yan Bindiga Fulani da aikatawa.

Babban Limamin kirista, Rev. Polycarp Lubo ne ya jagoranci zanga-zangar wadda aka fara ta daga Titin Fawvwei Junction wanda hakan ya kawo tsaikon ababen hawa.

Daya daga cikin masu zanga-zangar me suna Gyang Dalyop ya shaidawa kafar Punchng cewa, sun fito ne saboda basa jin dadin abinda ke faruwa na kashe-kashen a garuruwansu.

Itama wata me suna Hannatu Philip tace suna kira ga hukumomi su dauki matakan kawo karshen lamarin kamin ya kazance.

Karanta Wannan  Daliba 'Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar

A wani lamari me alaka da wannan, Hutudole ya kawo muku cewa, a yau ne ake sa ran mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *