Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu da dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara sun gana a Landan

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da dakataccen Gwannan jihar Rivers, Simi Fubara sun gana a jihar Landan.

Rahoton yace sun yi ganawar ne dan samo hanyar da za’a samu zaman lafiya a jihar ta Rivers.

Wannan ne karon farko da aka yi ganawa tsakanin Gwamnan jihar Rivers din da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tun bayan da ya dakatar dashi ya saka dokar ta baci a jihar.

Wani hadimin shugaba Tinubu ne ya bayyana hakan.

Saidai ganawar an yi tane ba tare da tsohon Gwamnan jihar Rivers ba watau Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Ana tsammanin dai shugaba Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki na jihar Rivers nan gaba.

Karanta Wannan  Wata Kungiyar masu ikirarin Jìhàdì ta je kusa da Abuja ta kafa sansani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *