
Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya kai ‘yansanda na musamman duka jihohin Najeriya dan su yaki ‘yan Bindigar da ake fama dasu.
Ya bayar da umarnin cewa kwamandojin ‘yansanda na Squadron da su shirya runduna ta musamman ta ‘yansanda na karta kwana wanda da an bukacesu a kowane lokaci zasu iya kai dauki.
Ya bayar da umarnin ne a zaman ganawa da kwamandojin ranar Talata biyo bayan hare-haren da ‘yan Bindiga suka kai jihohin Kwara, Benue da Sokoto suka kashe mutane 21.
Hakanan an samu kazaman hare-hare a jihohin Borno, Enugu da Filato.