Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawar da tawagar ta yi da shugaban ƙasar a Aso Rock Villa, a ranar Talata.