Monday, May 19
Shadow

GWAMNATI ZA TA BA MAHAJJATA KUƊIN GUZIRINSU A HANNU

Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.

Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ta ce shi ne ya nema wa mahajjatan sauƙin daga Babban Bankin Najeriya CBN.

“An bayyana damuwa game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025,” in ji sanarwar da Stanley Nkwocha ya fitar.

Ta ambato kwamashinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na hukumar alhazai, Aliu Abdulrazaq, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.

Karanta Wannan  Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin 'ƙauyawa' a jihar Kano

“Tun kafin yanzu mun sha yin ganawa game da kuɗin guziri a aikin Hajjin na 2025. Daga baya mataimakin shugaban ƙasa ya shiga lamarin kuma ya nemi alfarmar CBN,” a cewar kwamashinan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *