Tuesday, August 18
Shadow

Yanda Atiku Abubakar yayi yunkurin tsigeni dan ya zama shugaban kasa>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo me murabus ya bayyana cewa mataimakinsa, Atiku Abubakar ya shirya tsigeshi dan ya sama shugaban kasa.

Yace Atiku ya kira taro a ofis dinsa dake fadar shugaban kasa lokacin shi Obasanjon baya nan.

Yace Atiku sun gana da Kakakin majalisa na wancan lokacin, watau Ghali Umar Na’abba inda ya bashi Naira Miliyan 5 sannan yace a fara shirin tsige Obasanjo.

Yace shi kuma a wancan lokacin shugaban ma’aikatansa na fadar shugaban kasa ya nadarmasa duk abinda aka tattauna ya bashi yaji.

Yace duk da haka Atiku bai hakura ba, yaci gaba da neman tsigeshi sannan aka rika daina mu’amala dashi aka rika samun Atiku a matsayin mataimakinsa.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kotu ta saurari karar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya shigar da ICPC da DSS a yau inda yake neman Jimullar Naira Biliyan 3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *